Labarina Kaddarar Rayuwa Lyrics

Rayuwa kaddara ce kowa da irin tashi (labarina)
Haka soyayya ke rabuwa sashi sashi (labarina)
Babu tsammani so yayi min tafiyar mashi (labarina)
Sha’anin so na da baqar wahala ba bin bashi (labarina)
Naso shi tamkar raina, Kamar bana son kaina
Akan haka baiyi Imani ya fasa butulce mini ba

Labarinaaaaa labarina (labarina)
Labarinaaaaa labarina (labarina)
Labarinaaaaa labarina
Rayuwata in bake toh tamkar mutuwa ceee
Manufata mai kyawu ce akanki karki makance
Nasarata zata guje ga lokaci a kurace
Na dai laifi na tuba ki yafemin (labarina)
Banson harafi wanda zaisa ki gujemin (labarina)
In kika tafi so za ya sire min (labarina)
Bansamu baaa kamarki a tarin yammata
Ban sare baaa a sonki inada matserata
Ban shirya baaa na barki akwai tarin wawta

Kina sonaaa nima inasonki, kinsani
Labarinaaaaa labarina
Labarinaaaaa labarina
Gane masoyin gaske wannan sai Allah
A fuska a nuna ma so a zuciya akwai illa
Wasu nayin so don biya na buqantansu (labarina)
Basa duban me zai taba qimarsu (labarina)
Furucin qaryaaa ya zama halinsu (labarina)
Bai goge ba tabon da ya raunana zuciya ka barmin
Ban mance baa na riqe sakayya kayi min
Ban shirya ba don Allah ka barni a ni daya na
Labarinaaaaa labarina
Labarinaaaaa labarina